28 Mayu 2020 - 05:07
Shafin Twitter Ya Alamta Sakwannin Trump Da Na Yaudara

Karon farko shafin sada zumunta na twitter, ya alamanta wasu sakwannin shugaba Donald Trump, na Amurka a matsayin na yaudara.

(ABNA24.com) Karon farko shafin sada zumunta na twitter, ya alamanta wasu sakwannin shugaba Donald Trump, na Amurka a matsayin na yaudara.

Saidai tuni Trump, ya danganta matakin da barazana ga ‘yancin fadar albarkacin baki, wanda kuma a cewarsa a matsayinsa na shugaba ba zan lamunce wa hakan ba.

A martanin da ya mayar Trump, ya kuma zargi shafin na twitter da shishigi a harkokin zaben Shugaban kasar Amurka na 2020.

Wannan takkadamar data barke tsakanin Trump da shafin na twitter, ta biyo bayan da akayi ta sukan shafin na twitter kan yadda yaki cewa uffan kan zargin da shugaban na Amurka, ya yi wa wani tsohon zababen wakili da kashe wata mai hidima ta majalisa ba tare da wata hujja ba.

An dai jima da ake zargin twitter, da sakaci kan wasu kalaman da shuwagabain duniya ke wallafawa a shafin.

Trump, ya ce an yi magudi a shafin na twitter, wajen alamanta sakwannin nasa dana yaudara.


/129